ABNA24 : Kasashen sun sanar cewa sun dau wannan matakin ne saboda dalilai na kiyayewa, biyo bayan bayyanan cewa ana samun daskarewar jini ga mutanen da akayi wa riga kafin na AstraZeneca.
Kuma kasashen sun ce suna kan jiran rahoton da hukumar magunguna ta turai da ake sa ran za’a fitar yau Talata.
Saidai kamfanin harhada magungunan na hadin guiwar Ingila da Sweden, ya ce kawo yanzu babu wata hujja mai hadari, ta daskarewar jini da riga kafin kan haifarwa.
To saidai Yayin da manyan kasashen suka dakatar da amfani da rigakafin na AstraZeneca saboda rahotannin illar da aka ce yanayi, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce bata ga wata illah da maganin yake da shi ba kawo yanzu.
342/